Siyasa

2023: Babu Mara Lafiya Da Za’a Bar Shi Ya Zama shugaban kasa – Ƙungiyar Arewa

Kungiyar siyasa da zamantakewa ta Apex Northern Socio-Political Forum, Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana damuwarta kan yanayin lafiyar tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, bayan ya bayyana niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Advertisement

Kungiyar ACF, a wani taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna ranar Asabar, ta ce zai zama bala’i ga Najeriya idan aka tashi daga shugaban kasa da ke tafiya Turai neman lafiya zuwa wani da ke cikin irin halin da yake ciki.

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai, Sakataren Yada Labarai na Kasa, ACF, Emmanuel Yawe, ya bukaci “duk mutumin da yake da gamsasshen rahoton likita dake nuna cewa Mista Tinubu ya cancanci tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba to ya fito ya yi magana kafin lokaci ya kure.

Advertisement

Wadanda ke da shaidar cewa tsohon gwamnan Legas ba shi da lafiya, ya kamata su ceci yan Najeriya radadin rashin lafiyar shugaban kasa bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Idan mutane suna da batutuwa ko shaida game da lafiyar Tinubu, bari su fito su yi magana. Su ba da shaidar cewa bai isa ya tsaya takarar Shugaban kasa ba ko kuma ya rike mukami,” in ji Yawe.

“Mutanen da ke da shaidar cewa Tinubu bai isa rike ofishin Shugaban kasa ba, ya kamata su cece mu da radadin samun Shugaban kasa mara lafiya a ofis, su yi magana.

“Babban ofishi ne da zai tantance makomar miliyoyin ‘yan kasar nan. A cikin kasa mai sarkakiya kamar Najeriya, bai kamata mu bar wani da bai dace da ba ya mamaye irin wannan ofishi ba, sannan ya bata mu duka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari kullum yana fita kasar waje neman lafiya, kuma ‘yan Najeriya sun rika shirya zanga-zanga domin tilasta masa komawa gida. Gaskiya abin kunya ne. Kada mu bar irin wadannan abubuwa su sake faruwa,” in ji kungiyar.

Advertisement