Siyasa

2023: Atiku yayi tsufa ga tsayawa takarar Shugaban kasa – Afegbua

Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Edo, kuma tsohon mai taimakawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Kassim Afegbua, ya yiwa tsohon mai lamba biyu shakku kan damar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 saboda tsufa.

Afegbua, mamba a gidauniyar jam’iyyar PDP a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi bayan wani taron manema labarai a Abuja, yace PDP za ta harbi kanta a kafa idan har ta bai wa Atiku tikitin takarar shugaban kasa, yana mai cewa cin mutunci ne kawai yin haka da rashin amfani ga ƙwararrun ƴan takara.

Afegbua ya kuma bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya manta da burinsa na kashin kansa, ya kuma marawa wani matashi dan takarar daga shiyyar Kudu maso Gabas baya a 2033.

Advertisement

“Bayan kammala babban taron jam’iyyar PDP, tare da sabon shugabanci mai cike da alfanu, jam’iyyar za ta tashi tsaye wajen samar da dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudancin kasar nan domin kammala wannan aikin,” in ji Afegbua a cikin sanarwar.

Advertisement