Siyasa

2023: APC ba za ta wargaje bayan mulkin Buhari ba – Gwamna Badaru

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, yace jam’iyyar APC za ta cigaba da kasancewa tare da hadin kai har bayan wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a wani shirin a gidan Talabijin na Channels Television.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga rade-radin da yan adawa ke yi na cewa jam’iyya mai mulki za ta wargaje bayan shugaba Buhari ya bar mulki a 2023.

Advertisement

Ya bayyana cewa wasu gungun mutane ne suka kafa jam’iyyar APC a bisa dalili kuma shugaba Buhari ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar kuma daga karshe ya lashe zabe a shekarar 2015.

Yace wannan dalili ne zai sa APC ta kasance tare da hadin kai da karfi.

“Na san Shugaba Buhari a yau yana jagorantar abin da ya kamata a yi, don haka Obasanjo haka yake a PDP kuma lokacin da ya tafi ta wargaje? Don haka, idan Buhari ya bar mulki, ba zai yi kasa a gwiwa ba.

“Kuma Buhari zai kasance tare da mu, shine shugaban jam’iyyar kuma zai cigaba da kasancewa tare da mu.

Su kuma wadanda suka yi imani cewa Shugaba Buhari zai je Daura ne kawai ya kwana, ba su san shi ba, yana da kishin kasa, ya dawo mulki ne bayan ya yi kokari har sau uku saboda yana son abin ya canja.

“Don haka ba zai nade hannunsa ya bar abin da ya gina ko ya fara ginawa ya watse ko ya ruguje ba, kishin kasa a cikinsa ba zai bari haka ba, don haka muna da shugaba har yanzu,” in ji Badaru.

Advertisement