Siyasa

2023: Ƴan Arewa Tinubu za su zaba shugaban kasa – Gwamna Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce al’ummar yankin Arewacin kasar nan ba su da wani dan takarar shugaban kasa da za su mara wa baya kamar jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Advertisement

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da ofishin ƙwararrun matasan Arewa na Tinubu, (ƙungiyar da ke goyon bayan aniyar Tinubu ya zama shugaban ƙasa) wanda aka gudanar a Hadeja Road Kano ranar Litinin.

Advertisement

Advertisement