2007: Na San Yar’adua Bashi Da Lafiya Kafin In Goyi Bayan Sa – Obasanjo

, , Leave a comment

Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana sane da cewa Ummaru Musa Yar’adua bashi da lafiya gabanin ya goyi bayan sa a matsayin dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jami’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a zaben 2007, kamar yanda jaridar The Nation Nigeria ta ruwaito.

Amma kuma Obasanjo yace ya samu shawarar masana harkar lafiya cewa Yar’dua duk da anyi masa dashen koda, zai yi yin aiki a matsayin shugaban kasa.

READ ALSO:  Dalilin Da Yasa Muke Barin Matasa Matuka Suna Tuka Shugaban Sojoji Cikin Jirgi – NAF

Yar’adua wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2007, ya mutu ne a cikin watan biyar (5) a 2010.

Obasanjo wanda yayi magana a yau lahadi a wajen wata inta-biyu, ya musanta cewa ya kawo dan takara mai rauni a 2007 domin cinma wata bukatar kan sa.

“A wani lokaci na kamfen kafin zabe, zan yi tunawa Yar’adua yaje wajen duba lafiyar sa a kasar waje, wanda har ta kai bai halarci kamfen na jahar Ogun ba, inda aka yi ta cewa ya mutu, ni (Obasanjo) na kira shi (Yar’adua( da waya na saka lasifika inda na tambaye shi cewa ya mutu ko yana raye a gaban jama’a, kuma ya shaida min yana nan da ran shi, kowa yana ji.” Inji Obasanjo.