1966: Ɗan Kwallon Da Ya Taɓa Zura Ƙwalleye 3 A Gasar Cin Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe

Dan wasan gaba na Ingila Sir Geoffrey Hurst mai ritaya shi ne dan wasa daya tilo da ya zura kwallo a raga a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na maza.

Ya zura kwallaye uku a wasan da Ingila ta lallasa Jamus ta Yamma da ci 4-2 a filin wasa na Wembley a gasar cin kofin duniya a shekarar 1966.