Siyasa

Ƴan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a Osun

Rundunar yan sandan jihar Osun ta tabbatar da kashe Cif Gbenga Ogbara, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Atakumosa ta gabas ta tsakiya a jihar.

Kakakin Rundunar, SP. Yemisi Opalola, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin a Osogbo cewa wasu bindiga ne suka kashe shugaban da misalin karfe 12:00 na safe a dakin shi.

Opalola yace an ajiye gawar shugaban a asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo (OAUTH), Wesley Guild, Ilesa.

A cewar ta, ana cigaba da binciken yan sanda kan lamarin.

NAN ta samu labarin cewa yan bindigar sun kai farmaki gidan marigayi shugaban jam’iyyar APC da ke garin Igangan a mahaifar shi da misalin karfe 12:00 na safe inda suka harbe shi har lahira.

An tattaro cewa kisan na da alaka da siyasa domin zaben gwamna a jihar bai wuce watanni uku ba. (NAN).

Advertisement