Ƙasar Chadi Ta Miƙa Tsohon Shugaban Yan Tawayen Afrika Ta Tsakiya Ga kotun ICC

Hukumomin kasar Chadi sun mika tsohon shugaban mayakan yan tada kayar baya na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ake zargi da laifukan yaki da cin zarafin bil adama ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.

A ranar Litinin, kotun da ke Hague ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa Maxime Jeoffroy Eli Mokom Gawaka, wanda ake zargi da aikata laifuka a 2013 da 2014 “a Bangui da sauran wurare a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya,” yanzu yana hannun ta.

A shekara ta 2013, CAR ta shiga cikin rikici lokacin da wata gamayyar yan tawaye da ake kira Seleka ta hambarar da shugaba Francois Bozize, wanda akasari daga musulmi tsiraru ne.

Juyin mulkin ya haifar da zubar da jini na bangaranci tsakanin yan tawayen Seleka da na “Anti-balaka”, wadanda galibin su Kiristoci ne ko kuma masu tsaurin ra’ayi.

Mokom shi ne shugaban wata kungiya ta “Anti-balaka”.

A shekarar 2019, ya zama ministan kwance damarar makamai da fasa kwaurin makamai na kasar.

Kotun ta ICC ta ce ta sami wasu dalilai masu ma’ana don zargin cewa Mokom, a matsayinsa na “Mai Gudanar da Ayyuka na Anti-balaka”, yana da alhakin laifukan cin zarafin bil’adama, ciki har da kisan kai, azabtarwa, zalunci da kuma “bacewar tilastawa”.

A fagen laifuffukan yaki, ana zarginsa da, da wasu abubuwa, “da gangan ya jagoranci kai hari kan fararen hula” da kuma kai hari kan jami’an agaji da kuma shigar da mayaka ‘yan kasa da shekaru 15.

“Hukumomin Jamhuriyar Chadi sun mika Mr Maxime Jeoffroy Eli Mokom Gawaka ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa saboda sammacin kama shi da kotun ICC ta bayar a ranar 10 ga watan Disamba 2018,” in ji kotun.

“Bayyanawar Mista Mokom… zai faru nan da nan,” in ji sanarwar.

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, da ke birnin Hague, an kafa ta ne a shekara ta 2002 domin yi wa mutanen da aka gurfanar da su gaban kuliya bisa laifukan yaki, laifuffukan cin zarafin bil adama ko kuma ayyukan kisan kare dangi.

Tsofaffin shugabannin Anti-balaka guda biyu, Patrice-Edouard Ngaissona da Alfred Yekatom, tuni suna fuskantar shari’a a kotun ICC. A watan Satumba, wani da ake zargin shugaban Seleka zai gurfana a gaban kotun ICC domin fuskantar irin wannan tuhuma.

Madogara: Reuters.