Tsaro

Ɗalibai 4 da Aka Sace A Jami’ar Nasarawa Sun Sake Samun Ƴanci

Daliban hudu da aka sace na Jami’ar Tarayya ta Lafia, Nasarawa, sun samu ‘yanci.

Da yammacin ranar Asabar ne wadanda suka yi garkuwa da su suka sako daliban.

Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da mutanen hudu a ranar Alhamis din da ta gabata

Advertisement

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Shehu Abdul Rahman ya yabawa gwamnatin jihar Nasarawa da sauran jama’a bisa goyon bayan da suka bayar a lokacin.”

Advertisement