Siyasa

Ƴan Takarar Gwamna Biyu Sun Fice Daga APC Zuwa PDP Cikin Awa 48

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, yace jam’iyyar PDP ta kasance babbar jam’iyyar siyasa a Afirka da ke goyon bayan ‘yan Nijeriya a kowane lokaci baya ga mai tunani, girman kai, da juriya.

Arewa Times Hausa ta ruwaito cewa Mohammed na magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin jiga-jigan jam’iyyar APC a karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin jihar kuma dan takarar gwamna a jihar a 2023, Alhaji Mahmoud Maijama’a a daren ranar Talata a gidan gwamnati dake Bauchi.

Mohammed yace gwamnatin shi ta samar wa ‘yan kasa shugabanci nagari da ribar dimokuradiyya baya ga bullo da tsare-tsare da nufin inganta rayuwa da kuma sauya tarihin jihar.

Advertisement

A yayin da yake karbar wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, gwamnan ya yi kira gare su da su marawa kudirin gwamnatin shi na tallafa wa matasa da mata a fadin jihar a kokarinsu na samarwa da tallafa wa sana’o’insu domin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar Bauchi.

Haka zalika, Yusuf Lasun tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai a ranar Laraba ya koma jam’iyyar PDP a hukumance.

Lasun ya halarci taron shugaban kasa na jam’iyyar PDP a filin wasa na garin Osogbo.

Dan shekaru 62 ya tsaya takarar gwamnan jihar Osun a zaben 2022 a karkashin jam’iyyar Labour.

Ademola Adeleke ya zo na daya a zaben; Gboyega Oyetola na APC ya zo na biyu; Kehinde Atanda na Action Democratic Party (ADP) ya zo na uku; yayin da Lasun ta zo ta hudu.

Lasun dai ya kasance dan jam’iyyar APC ne har zuwa watan Fabrairu inda ya fice daga jam’iyyar bayan ya rasa tikitin takarar gwamna a jam’iyyar.

Advertisement