Tsaro

Ƴan ta’adda sun kashe mutum 5, sun kona tankar mai dauke da lita 33,000 akan hanyar Brinin Gwari/Kaduna

Yan ta’adda sun sake kashe mutane 5 a kauyen Manini da ke kusa da Kuriga, a kan hanyar Brinin-Gwari zuwa Kaduna mai ban tsoro.

Yan ta’addan sun kuma kona tankar mai da ke kai litar man fetur 33,000 zuwa Brinin-Gwari.

Shugaban kungiyar Brinin-Gwari Vanguard mai kula da harkokin tsaro da kyakkyawan shugabanci, Alhaji Ibrahim Abubakar Nagwari, a wata sanarwa da ya fitar, yace wadanda aka kashe sun hada da Saifudeen Lawal Isa da wasu yan asalin yankin Brinin-Gwari.

Advertisement

Yace yan ta’addan sun kashe mutum daya dan Kuriga da wasu biyu daga Udawa.

“Abin takaicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yamma inda yan ta’addan suka bude wuta kan masu ababen hawa a kan babbar hanyar sau 3. Yan ta’addan sun jikkata mata biyu da wasu biyar,” inji shi.

Advertisement