Tsaro

Ƴan sandan Najeriya sun cafke Abba Kyari, bayan NDLEA ta sanar da neman shi ruwa jallo

Jami’an rundunar yan sandan Najeriya sun kama dakataccen shugaban rundunar yan sandan farin kaya (IRT) DCP Abba Kyari, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An kama shi ne tare da wasu mutane hudu a ranar Litinin bisa zargin shi da alaka da ƙungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Kamen dai ya zo ne sa’o’i bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin alaka da miyagun kwayoyi.

Advertisement

Ana kuma ci gaba da gudanar da binciken ‘yan sanda bayan da hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka FBI ta tuhume shi da laifin zamba da ya shafi wani shahararran shafin Instagram, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Wani kwamiti na musamman da IGP Usman Alkali ya kafa ne ya binciki rahoton, wanda kuma ya mika shi ga babban mai shari’a na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, domin samun shawarwarin shari’a.

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta baiwa ‘yan sandan wa’adin makonni biyu su kammala bincike kan lamarin da ya shafi Kyari.

Advertisement