Laifuku

Ƴan Sanda Sun Yi Ram Da Wasu Ma’aurata Da Suka Binne Jaririn Da Suka Haifa Da Ran Shi

Wata mata ‘yar shekara 30, wadda ta binne jaririn da ta haifa da rai, ta amsa laifin da ta aikata, inda ta ce cikin ba a son shi tun farko.

Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa sun cafke wata mata mai suna Balaraba Shehu mai shekaru 30 tare da mijinta Amadu Sale bisa laifin binne jaririn da aka haifa a raye.

An ce masoyan sun aikata laifin ne a karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.

Advertisement

Da yake bayyana kamen ma’auratan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Adam, yace an kama su ne biyo bayan rahoton da ake zargin matar ta haihu ta binne sabon jaririn.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa da samun rahoton, an tattaro tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru.

A cewar Adam, da isar su jami’an sun zage damtse inda suka fito da jaririn da aka haifa a bayan gida, inda mahaifiyar da ake zargin ta binne shi.

Sai dai an tabbatar da mutuwar jaririn a babban asibitin Dutse, inda aka garzaya da shi.

Adam yace binciken farko da aka yi ya nuna cewa mahaifiyar ta binne jaririyar tare da bayyana cewa cikin ba’a son shi wanda a karshe ya kai ga kama Sale, wanda aka fi sani da Dan Kwairo.

Ana zargin Dan Kwairo ne da hannu wajen yi wa matr cikin da bai so ba, kuma ya hada baki wajen binne jaririn bayan ta haihu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan, yace kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Emmanuel Effiom, ya bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa sashin bincike na rundunar (SCID) da ke Dutse, domin gudanar da bincike mai zurfi.

Ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin su fuskanci fushin doka da zarar an kammala bincike.

Advertisement