Tsaro

Ƴan sanda sun tabbatar da kashe mutane 16 a harin Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi a ranar Litinin ta tabbatar da kisan mutane 16 da ‘yan bindiga suka yi a kauyen Dankade da ke karamar hukumar Danko/Wsaagu ta jihar.

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 50 ne aka kashe a harin na ranar Juma’a a kauyen.

Kakakin rundunar, Nafi’u Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Birnin Kebbi, ya ce dan sanda da sojoji biyu na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Advertisement

Ya ce ‘yan bindigar sun kuma kona wasu gidaje a cikin al’umma.

Abubakar ya ce: “An kashe fararen hula 13 sannan mun kuma kawar da wasu ‘yan bindiga da ba a san adadinsu ba a cikin fadan.”

Advertisement