Al'umma

Ƴan sanda sun tabbatar da gano gawarwakin mutane 20 a kogin Kenya

KENYA – Rundunar yan sanda a kasar Kenya a ranar Laraba ta tabbatar da gano gawarwaki sama da 20 a kogin Yala da ke yankin Kisumu da ke arewa maso yammacin kasar.

Kakakin hukumar yan sanda ta kasa (NPS), Bruno Shioso, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kwashe shekaru biyu ana zubar da gawarwakin a cikin kogin.

Ya ce: “An kwashe shekaru biyu ana tsintar gawarwakin gawarwakin da aka gano daga kogin da ke yammacin kasar.”

Advertisement

Ya ce har yanzu bincike bai gano wadanda ke da hannu ko kuma musabbabin kisan ba.

Masu fafutukar kare hakkin bil’adama a kasar da ke gabashin Afirka a ranar Talata sun koka kan yadda masunta na yankin suka kwato gawarwaki 20 a cikin kogin.

An ajiye gawarwakin a buhu aka jefa cikin kogin.

Daga baya aka dauko su aka kai su dakin ajiye gawa na Asibitin Yala domin a tantance su.

Advertisement