Tsaro

Ƴan sanda sun karyata zargin cewa shugaban ƴan bindiga, Turji ya koma Kwara

Rundunar yan sandan jihar Kwara ta musanta rahotannin da ke cewa shugaban yan bindigar jihar Zamfara, Bello Turji, ya gudu zuwa wani dajin da ba a san ko ina ne ba a jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan, Okasanmi Ajayi, ya fitar a Ilorin ranar Laraba, tace bayanin ya zama dole don kawar rikicin da wasu kalamai da aka danganta ga wani dan majalisar tarayya a majalisar wakilai suka riga suka haifar a zukatan jama’a cewa shugaban da yan kungiyarsa sun koma wani daji da ba a san ko a ina ne ba a jihar Kwara.

Sai dai sanarwar da dan majalisar ya fitar ba ta bayyana tushe ko sahihancin furucin nata ba,” in ji kakakin yan sandan, yana mai ba da tabbacin cewa “Jihar Kwara na cikin koshin lafiya.”

Advertisement

Okasanmi yace “Dukkan iyakoki, na gida da na waje a cikin jihar, yan sanda da sojoji sun tsare su sosai.

Yan banga da mafarauta na gida suna aiki tukuru tare da jami’an tsaro don ganin an kula da dazuzzukan mu da kuma kare lafiyar su,” ya kara da cewa.

Kakakin ya bayyana cewa, kwamishinan yan sandan jihar, Tuesday Assayomo, ya bayar da umarnin gudanar da sintiri na sa’o’i 24 na dukkan wuraren shiga da fita zuwa jihar, yayin da aka sake karfafa rundunonin dabarun yaki tare da samar da karin motocin sintiri da sauran kayayyakin aikin da ake bukata da kuma karfafa gwiwa da taimaka aikinsu.

Kwamishinan ya kuma shawarci jama’a da su rika ba jami’an tsaro bayanai na ban mamaki motsi da abubuwan da ke kewaye da su ga jami’an tsaro a kowane lokaci.

Jita-jitar sarkin yan fashin, Bello Turji da yan kungiyarsa ta yi kamari inda aka ce ya koma jihar Kwara, biyo bayan farmakin da jami’an tsaro suka kai maboyarsu a jihar Zamfara, a kwanakin baya.

Advertisement