Al'umma

Ƴan sanda sun dawo da zaman lafiya bayan mutanen kauye sun kashe wasu masu garkuwa da mutane

Biyo bayan rikicin da ya dabaibaye garin Mangun da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, rundunar yan sanda a jihar a ranar Asabar ta ce ta maido zaman lafiya.

Advertisement

An samu tashin hankali a garin Mangun da kewaye tun ranar alhamis lokacin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka abka cikin al’ummar tare da yin garkuwa da dan wani dan kasuwa.

An ce mutanen kauyen sun hada kansu tare da fatattakar wadanda ake zargin.

Advertisement

An tattaro cewa wasu fusatattun mutane sun hallaka biyu daga cikin masu garkuwar bayan an kama su.

An kuma ce wadanda ake zargin sun harbe daya daga cikin mutanen kauyen a lokacin da lamarin ya faru.

Daga baya lamarin ya tabarbare a lokacin da mutanen kauyen da suka yi wa garkuwa da mutane kawanya suka gano cewa daya daga cikin wadanda ake zargin Bafulatani ne.

Majiya mai tushe ta ce mutanen kauyen daga nan ne suka yi kaca-kaca inda suka fara cinnawa wasu gidaje da ake zargin na Fulani ne wuta sannan su ma Fulanin sun mayar da martani wanda ya kai ga tauye doka da oda a yankin.

Advertisement