Tsaro

Ƴan sanda sun dakile harin yan ta’adda, tare da kwace babura 6 a Katsina

Jami’an yan sanda a jihar Katsina sun ce sun dakile wani harin da yan ta’adda suka kai kauyen Barewa da ke karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina, inda suka kwato babura 6 na ƴan bindiga.

Advertisement

Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

A cewar SP Gambo, an ga yan ta’addan da suke kan babura da yawa, dauke da bindigogi kirar AK-47, yayin da suke kan hanyar su ta zuwa kauyen Barewa kuma an sanar da yan sanda.

Advertisement

A martanin da aka mayar, an tattaro tawagar yan sanda da sojoji zuwa yankin, inda suka yi artabu da yan ta’addan cikin wani mugunyar bindigu tare da samun nasarar fatattakar su, inda yan ta’addan suka tsere saboda dabarun gudanar da aiki da gallazawar da jami’an tsaro suka nuna.

SP Gambo ya ce, a ci gaba da binciken inda lamarin ya faru, rundunar ‘yan sandan ta gano baburan ‘yan fashi guda biyar tare da kone su, yayin da jami’in ‘yan sanda na Batagarawa suka kwato wani babur na ‘yan fashin da suka yi watsi da su a dajin Barawa.

A cewar SP Gambo, da yawa daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Advertisement