Al'umma

Ƴan Sanda Mata 2 Sun Mutu, Wasu 17 Sun Jikkata A Wani Haɗari Da Ya Rutsa Da Motocin Ƴan Sanda

Jami’an ‘yan sanda biyu na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ‘yan sandan Najeriya mai suna Godiya da PC Kubra sun rasa rayukan su yayin da wasu 17 suka samu raunuka daban-daban a wani hadarin mota da ya rutsa da su.

SaharaReporters ta tattaro cewa hatsarin ya afku ne a hanyar Jos, jihar Filato a ranar Litinin yayin da jami’an ‘yan sandan ke kan hanyar su ta zuwa jihar Akwa Ibom domin gudanar da wasannin ’yan sanda karo na 13 da ke tafe, UYO 2022.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Sani kamilu Shatambaya, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A wata tabbatarwa, kakakin rundunar ‘yan sandan ya aikewa SaharaReporters, yace, “Kwamishanan ‘yan sandan jihar Borno, ya yi nadamar afkuwar lamarin da ya faru ga tawagar ‘yan sandan da ke wakiltar shiyya ta 15 da ta kunshi rundunar ‘yan sandan jihohin Borno da Yobe a kan hanyar su ta zuwa taron. Wasannin ‘Yan Sanda Biyual 2022 a Uyo, Jihar Akwa Ibom.

Advertisement