Siyasa

Ƴan Najeriya Da Suka Yi Rajista A 2022 Nan Ba Da Jimawa Ba Za Su Karbi Katin zaɓen Su – INEC

A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce nan ba da dadewa ba za ta fitar da jadawalin lokaci da tsarin da za a yi na karbar sabbin katunan zabe na dindindin (PVCs).

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a taron masu ruwa da tsaki na kungiyar ‘Nigerian Civil Society Situation Room (CSSR)’ a Abuja.

Shugaban na INEC ya bayyana cewa hukumar ta samu cigaba wajen samarwa da kuma kai kayan zabe masu muhimmanci da marasa hankali ga ofisoshinta na jihohi.

Advertisement