Tsaro

Ƴan majalisar dokokin Rasha sun ba Putin izinin amfani da sojoji a ƙasashen ketare

A ranar Talata ne yan majalisar dokokin Rasha suka kada kuri’ar amincewa shugaba Vladimir Putin ya yi amfani da sojojin Rasha a wajen kasar wajen tallafawa yan aware a Ukraine.

Sanatoci 153 na Rasha ne suka goyi bayan matakin, ba tare da wani wanda ya ki amincewa da shi ba ko kuma ya kaurace masa, inji NDTV.

Duk da cewa a baya ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ba sa shirin tura sojoji zuwa gabashin Ukraine “a halin yanzu,” Putin ya bukaci majalisar tarayya da ta amince da amfani da sojojin a wajen kasar domin marawa ‘yan awaren da ke yaki da sojojin Ukraine tun shekara ta 2014.

Advertisement

“Tattaunawar ta ci tura. Shugabancin Ukraine ya dauki hanyar tashin hankali da zubar da jini, “in ji mataimakin ministan tsaro Nikolay Pankov a wani zama na Majalisar Tarayyar da aka kira bisa bukatar Putin.

“Ba su bar mana zabi ba,” in ji Pankov, yayin da yake jawabi ga zauren.

Ya yi zargin cewa akwai “manyan motoci masu sulke” a kan iyakar gabashin Ukraine da ke karkashin ikon ‘yan aware da ake kira DNR da LNR.

Pankov ya kuma ce NATO tana “taimakawa Ukraine da makamai na zamani.”

Pankov ya ce “Rasha za ta yi aiki don kare ikon sauran jihohi da kuma hana ayyukan ta’addanci,” in ji Pankov.

Ya ambaci bukatar Putin: “Bisa ga yarjejeniyar abokantaka da haɗin gwiwa tare da DNR da LNR, Ina gabatar da shawarwari don amincewa da Majalisar Tarayya don amincewa da amfani da sojojin Tarayyar Rasha a wajen Rasha.”

A jiya litinin, Putin ya amince da ‘yancin cin gashin kan yankunan Donetsk da Lugansk tare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da aka kulla da su, lamarin da ya bude kofar kasancewar sojojin Rasha a yankunan ‘yan tawayen Ukraine.

Advertisement