Tsaro

Ƴan majalisar dokokin Amurka sun matsa wa Biden ya taimaka wajen tura jiragen yaƙin Turai zuwa Ukraine

MIG-29 fighter aircrafts

Yan majalisar dokokin Amurka sun matsawa gwamnatin shugaba Joe Biden a ranar litinin domin saukaka jigilar jiragen yaki zuwa Ukraine daga Poland da sauran kasashen kungiyar tsaro ta NATO da kuma kasashen gabashin Turai, bayan rokon da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy yayi a ranar Asabar.

Fadar White House tace ba ta adawa da aikewa da jiragen sama zuwa Ukraine amma ta ga akwai kalubalen kayan aiki.

Shugaban kwamitin hulda da kasashen waje na majalisar dattijai Bob Menendez ya rubuta wa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sakataren tsaro Lloyd Austin suna kira ga Washington da ta himmatu wajen maye gurbin duk wani jirgin da aka bada gudummawa da ingantattun jirage na yammacin duniya, gami da tallafin kudade da lamuni da kuma farashin tallafi.

Advertisement

Ya kuma ce ya kamata NATO ta sake tura jiragen yaki zuwa duk wani sansani da aka ajiye jiragen da aka ba da gudummawa.

Zelenskiy yayi kira ga kasashen Turai da su samar da jiragen yaƙi sama wadanda Rasha kera don yakin da Ukraine ke yi da mahara Rasha a yayin wani taron bidiyo da yayi jiya Asabar tare da yan majalisar dokokin Amurka, inji mahalar ta kiran.

Da yawa daga cikin sojojin sama a Gabashin Turai suna shawagi da jiragen yaƙi na Rasha, kuma tura irin waɗannan jiragen zuwa Ukraine na nufin yan Ukraine za su iya tuka jiragen ba tare da ƙarin horo ba.

“Zan goyi bayan kokarin da ake yi a majalisar dattijai don aiwatar da matakan biya abokan mu da ke ba da jiragen su don kare Ukraine,” inji Menendez.

Advertisement