Tsaro

Ƴan bindiga sun sace mata da ɗiyar kwamishinan Muhalli, Usman Bamaiyi

Wasu yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi garkuwa da mata da diyar Kwamishinan Muhalli na Jihar Filato, Usman Bamaiyi.

Bamaiyi yana daya daga cikin masu neman tikitin takarar kujerar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa yan bindigar sun shiga gidan Gindiri na Bamaiyi da sanyin safiyar Asabar domin yin garkuwa da mata da yar shi.

Back to top button