Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Matar Basarake Da Ƴaƴan Shi Biyu A Kaduna

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da matar da ‘ya’yan shugaban kauyen Galadimawa da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Hussaini Umar, wani basaraken gargajiya kuma Sarkin Fada Galadimawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun isa kauyen da yawan gaske, inda suka rika harbe-harbe don tsorata jama’a kafin su tsallaka bango domin shiga gidan hakimin kauyen, suka yi awon gaba da ita matar, Fatima, da yayan shi, Abdullahi da Kamal.

“Ba mu cikin natsuwa a nan, domin matar Hakimin kauyen mu ta biyu, Alhaji Aliyu Haruna Galadimawa, da ‘ya’yansa guda biyu ‘yan bindiga sun sace su a lokacin da suka kai farmaki gidansa,” in ji Umar.

Ya bayyana cewa maharan sun mamaye gidan baki daya ciki har da silin bayan sun kutsa katangar, inda ya kara da cewa da ba su samu shugaban kauyen ba, sai suka yi awon gaba da matarsa ​​ta biyu da ‘ya’yan biyu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, bai amsa kiran sa ba, ballantana amsa sakonnin tes da aka aika masa domin tabbatar da faruwar lamarin.