Tsaro

Ƴan Bindiga Sun Sace Kwamishinan Gida Da Raya Garuruwa Da Wasu Mutane Uku

An yi garkuwa da kwamishinan gidaje da raya manyan garuruwa na jihar Benue, Mista Ekpe Ogbu.

An yi garkuwa da shi ne a hanyar Otukpo-Ado a karamar hukumar Ado ta jihar da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.

Mai baiwa gwamna Samuel Ortom shawara kan harkokin tsaro Kanar Paul Hemba (mai ritaya) ya tabbatar da sace kwamishinan ga gidan talabijin na Channels a daren Lahadi.

Advertisement

Yace motar da kwamishinan yake ciki ‘yan sanda sun gano motar da ke Otukpo, kuma an fara aikin ceto.

A cewar shi, har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi iyalan shi ba.

Sai dai a rahoton da jaridar The PUNCH ta wallafa, an yi garkuwa da Ogbu ne tare da wasu mutum uku – Honourable Agbo Ode, daya daga cikin surikinsa kuma direban motar.

An ce kwamishinan ya halarci wani taron coci inda Sanata Abba Moro mai wakiltar mazabar Benue ta Kudu ya sadaukar da sabuwar majalisar yakin neman zaben shi ga cocin St. Augustine Catholic Church, Otukpo.

Rahotanni sun ce Ogbu na zuwa kauyen shi ne da ke Ndekma a gundumar Utonkon bayan shirin cocin lokacin da aka yi garkuwa da shi da wasu. PUNCH ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:45 na daren Lahadi.

Advertisement