Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 7, Suka Sace Wasu Sama Da 100 A Katsina
Kimanin mutane bakwai ne aka kashe tare da yin garkuwa da aƙalla mutane 100 a daren ranar Asabar a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyukan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda mazauna yankin da ‘yan sanda suka bayyana a ranar Lahadi, a wani hari na baya-bayan nan da aka kai kan mazauna arewacin kasar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abubakar Aliyu Sadiq ya tabbatar da faruwar harin da kuma mutuwar mutane bakwai, sai dai ba zai bayyana ko akwai wanda ya bata ba. Ya ce ‘yan sanda na gudanar da bincike.
“Sauran mutanen da ba su gudu ba suna rayuwa cikin tsoro, kuma suna jiran su ji labari game da ‘yan uwansu da aka sace,” in ji Muhammad Sani, wanda aka sace ‘yar uwarsa.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar a kan babura sun isa kauyen Maidabino da ke cikin karamar hukumar Danmusa a Katsina, inda suka fara harbe-harbe a kai a kai, lamarin da ya tilastawa mazauna kauyen tserewa.
Hassan Aliyu ya shaidawa kamfanin dillancin labaran reuters ta wayar tarho cewa harin ya baiwa mazauna yankin mamaki kuma an tabbatar da batan mata da kananan yara da dama.
“Sun kashe mutane bakwai, ciki har da yara biyu suka kona,” in ji Aliyu. “Sun kwashe fiye da sa’o’i shida suna lalata mana kadarori.”
Auwalu Ismail, wani mazaunin garin ya ce ‘yan bindigar sun fara tare dukkan hanyoyin da ke zuwa Maidabino kafin su kai harin.
“Sun kona shaguna da ababan hawa, tare da kwashe dabbobin mu. Sun kuma yi garkuwa da matata da mata da yara sama da 100,” inji shi.
A shekarun baya-bayan nan dai, irin wadannan sace-sacen sun ta’allaka ne a yankunan arewa maso yammacin Najeriya da kuma tsakiyar Najeriya, inda kungiyoyi da dama da ke dauke da makamai sukan kai hari kan mazauna kauyuka da matafiya domin karbar kudin fansa mai yawa.
A cikin watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wata makaranta a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar inda suka yi garkuwa da dalibai da dama a lokacin da suke shirin fara karatu, kamar yadda mazauna yankin da hukumomin kasar suka bayyana.
Madogara: Al Jazeera