Siyasa

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin INEC, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ce ‘Babu Zabe A Lasar Biafra’

Hoto: Domin misali

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba da ake zargin Eastern Security Network, ESN ne, sun kai hari ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ke Jihar Imo, inda suka kashe mutum daya a cikin harin.

DAILY POST ta tattaro cewa ‘yan bindigar wadanda adadin su ya kai kamar 20, sun yi amfani da mota kirar SUV guda biyu, Lexus mai launin shudi daya da kuma Highlander mai launin ash.

Masu harbin sanye da rigar ESN, sun mamaye ofishin INEC da ke sakatariyar karamar hukumar Ahiazu, inda suke neman ma’aikatan da ke raba katin zabe na dindindin, PVC.

Advertisement

An ajiye gawar mai gadin da aka kashe a dakin ajiyar gawa.

Da wakilin DAILY POST ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Imo, PPRO, Henry Okoye, ya ce har yanzu bai ci gaba da aiki ba, amma ya nemi jin ta bakin tsohon PPRO, Mike Abatam, wanda ya ki cewa komai kan lamarin.

Advertisement