Tsaro

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci, Sun Harbe Liman, Sun Sace Mutane 18 Ana Sallar Isha’i

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya ranar Asabar, inda suka harbe wasu tare da yin garkuwa da wasu.

‘Yan ta’addan sun tarwatsa Sallar Isha’i a lokacin da suka kai hari a masallacin da ke cikin Jihar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Masallacin yana kauyen Maigamji ne a kan titin Funtua zuwa Dandume a karamar hukumar Funtua.

Advertisement

Wani tsohon kansila mai unguwar Maigamji, Alhaji Lawal Maigamji, ya ce maharan sun harbe mutane biyu ciki har da Limamin da ke jagorantar sallar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana wadanda aka harba a matsayin Limamin, Malam Yusha’u da kuma mai ibada, Hussaini Jamo, inda yace suna jinya a wani asibiti da ke Funtuwa.

“Sun kewaye masallacin ne a lokacin da ake gudanar da Sallar Isha’i. Bayan harbe Imam Yusha’u da Hussaini Jamo, sun yi awon gaba da mutane 18 tare da yin garkuwa da su cikin daji,” inji Maigamji.

Sai dai yace hudu daga cikin wadanda aka sace sun tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su a lokacin da suke wucewa.

Advertisement