Tsaro

Ƴan bindiga na cigaba da nuna turjiya saboda Buhari yana da rauni – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai ta 8, Sanata Shehu Sani, ya dora alhakin jajircewa da turjiyar yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma a kan rashin jajircewar shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen tunkarar su.

Yayin da yake mayar da martani game da kisan yan bindiga sama da 20 da sojojin Najeriya suka yi a lokacin da suka nufi makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA) a ranar Juma’a, Sani yace da Buhari yayi abin da ya kamata ta hanyar ayyana yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda da wuri kuma ya ba su irin mu’amalar da yan ta’adda suke yi da an ba su, da ba za su kasance suna aiki da irin ƙarfin hali da suke nunawa ba.

A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a ranar Asabar din da ta gabata ta bayyana cewa yan bindigar da yawans u ya haura 100, dauke da manyan muggan makamai, an hangi su a kan babura sun kama hanyar zuwa makarantar sojoji a ranar Juma’a da yamma, amma sun gamu da ajalin su yayin da wasu jiragen sojojin saman Najeriya biyu (NAF) da aka domin su tunkare su.

Advertisement

Yayin da yake mayar da martani ga labarin a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, Sani ya ce:

“Abin yabawa ne idan muka samu labarin cewa sojoji sun fatattaki ‘yan ta’addan da suke zuwa makarantar horas da sojoji ta Najeriya, Kaduna.

“Amma kuma ya nuna yadda masu aikata laifuka ke jajircewa da kuma irin hadarin da muke fuskanta a garinmu a halin yanzu.

“Jajircewarsu ta zo ne saboda shugaban kasa da kwamandan rundunar sun ki sanya su a matsayin ‘yan ta’adda tare da ba su ‘yan ta’adda magani.

“Ya kasance kuma yana da rauni idan ana maganar ‘yan fashi. Fadakarwa shine mabuɗin.”

Advertisement