Al'umma

Ƴan Ƙabilar Topossa Masu Tsaga A Jiki Don Al’ada

A Afirka, tsaga jiki ya zama muhimmin abu na al’adun kabilu daban-daban.

Tsaga ya ƙunshi sanya tsaga a jikin fata ta hanyar amfani da duwatsu, gilashi, wukake, ko wasu kayan aiki don ƙirƙirar hotuna, kalmomi, ko alamomi masu ma’ana.

Wannan gyare-gyaren jiki na dindindin zai iya zama sadarwa ko alama na abubuwan al’adu. Daga Habasha ta Ethiopia zuwa Papua New Guinea, tsaga yana haifar da tabo masu girma dabam, siffofi, da matsayi daban-daban don nuna asalin dangi, matsayi a cikin al’umma har zuwa girma.