Tarihin Ɗan Wasan Tunisia Hatem, Wanda Zura Ƙwallo 1 Kacal A Wasanni 66 Da Ya Buga

Tsohon dan wasan baya na Tunisia Hatem Trabelsi ya buga wasanni 66 na kasa da kasa kuma ya zura kwallo daya tilo da yaci a wasan sada zumunta da Ghana a shekarar 2006.

Ya halarci gasar cin kofin duniya sau uku a jere (’98, 2002 da 2006) kuma ya kasance memba mai mahimmanci a cikin ‘yan wasan da suka lashe kofin AFCON daya tilo a Tunisia a 2004.

A matakin kulob, ya fara taka leda ne da kulob din CS Sfaxien na Tunisiya, inda ya ke taka leda a matsayin gaba kafin raunin da ya samu ya sa aka mayar da shi baya na dama. Ya lashe kofin CAF da kofin zakarun kungiyoyin Larabawa a kulob din.

A 2001, ya shiga Ajax inda ya lashe gasar Eredivisie, Kofin KNVB da Johan Cruijff Shield. A shekarar 2003 ne aka zabe shi a matsayin wanda zai lashe kyautar ballon d’Or amma bai samu kuri’u ba.

A cikin 2004, Arsène Wenger ya ba shi lokacin gwaji a Arsenal. An amince da kudi tsakanin Ajax da Arsenal. Sai dai bayan an samu rashin jituwa kan biyan Trabelsi na albashi, Trabelsi bai kulla yarjejeniya da Arsenal ba ya ci gaba da zama a Ajax.

Ya koma Manchester City a kyauta a watan Agustan 2006 kuma ya ci kwallonsa ta farko a wasan Manchester derby wanda har yanzu Man City ta sha kashi da ci 3-1.

Ya bar kulob din zuwa Al-Hilal a shekara ta gaba kafin ya yi ritaya a 2008.