Siyasa

Ƙungiyar alkalan ƙasar Tunisia ta yi kira da a gudanar da zanga-zanga

Ƙungiyar Alkalai ta Tunisia ta yi kira a ranar Talata don gudanar da zanga-zanga a ranar 24 ga watan Fabrairu nan domin mayar da martani ga cigaba da kai wa hukumomin shari’ar kasar Tunisia hari, inji wata sanarwa da ta fitar.

Shugaban Tunusiya Kais Saied ya bayyana matakinsa na rusa majalisar koli ta shari’a a farkon watan Fabrairu tare da tsawaita dokar ta-baci a kasar har zuwa ranar 31 ga watan Disamba na wannan shekara.

Advertisement
Advertisement