Ƙudirin Kafa Wata Jiha, Adada A Yankin Kudu Maso Gabas Ya Wuce Karatun Farko
A ranar Talata ne kudurin dokar da ke neman samar da jihar Adada, wata jiha a shiyyar yankin Kudu maso Gabas, a ranar Talata ya wuce karatu na farko a majalisar dattawan Najeriya.
Kudurin wanda aka bayyana shi a matsayin “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Bill, 2024 (SB. 482)” ya samu goyon baya ne daga dan majalisar dattawa mai wakiltar Enugu ta Arewa Sanata Okey Ezea.
Kudirin, a cewar dan majalisar, yana neman gyara sashi na 3(1) da jaddawalin farko, sashi na 1 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya domin bada damar kafa wata jiha a yankin Kudu maso Gabas.
An dauki wannan mataki ne da nufin maida adadin jihohin yankin zuwa shida kamar yadda ake yi a wasu shiyyoyin siyasar kasar.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa tun a shekarar 1983 ne aka fara tada jijiyar wuya na samar da jihar Adada tun a shekarar 1983 lokacin da marigayi Sanata Isaiah Ani mai wakiltar mazabar Nsukka a jamhuriya ta biyu ya gabatar da kudirin dokar.