Nishaɗi

Ƙazafin Zina: Matan Kannywood za su maka Naziru Sarkin waƙa a kotun Musulunci

Ƙungiyar Matan Kannywood (Kannywood Women Association of Nigeria, K-WAN) ta bai wa fitaccen mawaƙin nan na Arewacin Najeriya Naziru M. Ahmad wa’adin kwana uku kachal da ya janye kalaman zargin da ya yiwa wasu daga cikin mata yan fim ko kuma su yi ƙarar sa a kotun Musulunci.

Wa’adin da Matan suka ɗebawa Sarkin Waƙa zai fara aiki ne daga yau Litinin, 14 ga Fabrairu, 2022.

Shugabar ƙungiyar, Hauwa A. Bello (Edita), ita ce ta bada wannan wa’adin a cikin wata takardar sanarwa da ta aika aikewa manema labarai a yau Litinin.

Advertisement

Idan zamu iya tunawa, Sarkin Waƙa (Naziru) ya wallafa wani bidiyo a shafin Facebook inda yayi zargin cewa ba’a sanya wasu jarumai mata a harkar fim a masana’antar Kannywood sai sun bada kan su an yi lalata da su.

Naziru yayi wannan zargin ne a lokacin da yake mayar da martani ga waɗanda su ka yi fatali da iƙirarin da dattijuwar nan yar wasan Hausa Hajiya Ladin Cima (Tambaya) ta yi inda ta ce ba’a taɓa biyan ta sama da ₦5,000 ba idan ta yi fim.

Naziru ya ware wasu jarumai kamar Ali Nuhu da Falalu Ɗorayi musamman a martanin na shi, yace babu tsoron Allah a zuciyar wasu yan fim.

Advertisement