Kasuwanci

Ƙasashen da ke sayen danyen man Najeriya, da kuɗin da suka kashe wajen sayen man

Yayin da kasashe da dama ke kauracewa sayen danyen mai na kasar Rasha, an bude sabuwar damar fitar da danyen mai na Najeriya wanda ake yiwa kallon daya daga cikin mafi inganci a kasuwar mai ta duniya.

Danyen mai na Najeriya kuma yana daya daga cikin mafi tsada kuma ana sayar da shi sama da dala $118 a karshen kasuwar ranar Juma’a.

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, a cikin wata makala ta shekara-shekara (ASB), ya bayyana cewa a cikin shekaru 10 ya samar da ganga biliyan ₦8.42 na mai tare da sayar da shi ga kasashe sama da 56.

Advertisement

Wadannan kasashe da ke sayen man Najeriya sune daga yammacin Turai, Oceania/Pacific, Kudancin Amurka, Arewacin Amurka, Gabas ta Tsakiya, Asiya da Gabas Mai Nisa da kuma Afirka.

A karshen, kididdigar cinikayyar kasashen waje, Ofishin Kididdiga na Kasa ya bayyana cewa a kashi na uku na shekarar 2021 Najeriya ta sayar da danyen mai na Naira Tiriliyan ₦4.02.

Indiya ce ta jagoranci masu siyan danyen man Najeriya a cikin Q3 2021 inda ta kashe ₦703.26bn sai Spain ₦544.59bn.

Italiya da Faransa sun biya Naira biliyan ₦442.11 da Naira biliyan ₦233.74 su biyun.

Kasar Netherland na daga cikin manyan kasashe biyar na sayan danyen man Najeriya sama da Naira biliyan ₦226.79 da aka biya a asusun gwamnatin tarayya.

Kasar Amurka da ta taba jagorantar teburin a yanzu tana matsayi na 6 inda ta kashe Naira biliyan ₦199.54 cikin watanni uku.

Indonesiya da Kanada da Ivory Coast da kuma Portugal ne suka zo na 10 da suka kai Naira biliyan ₦197.60, da Naira biliyan ₦202.03, da Naira biliyan ₦182.79, sannan kuma ke kan gaba da Naira biliyan ₦117.8.

Yayin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta bai wa Najeriya damar hako karin ganga 400,000 a wata mai zuwa zuwa jimillar kaso miliyan 1.73 a kullum, Najeriya na iya samun karin kudi.

Duk da cewa da wuya Najeriya ta samar da wannan adadin, amma idan bisa ga wani dalili ta cika kason da aka amince da ita, akalla biliyan ₦8 zai shiga cikin asusun gwamnati a kullum.

Advertisement