Labarai

Ƙasar Pakistan Ta Bayyana Isra’ila A Matsayin Ƙasar Ƴan Ta’adda

Pakistan ta sanar da kafa wani kwamiti da zai tantance kamfanonin da za su kauracewa saboda goyon bayan Falasɗinawa, inji Wafa.

“An kuma kafa wani kwamiti da zai zakulo irin wadannan kamfanoni da kayayyaki a Pakistan wadanda masu dangantaka da Isra’ila kai tsaye ko a fakaice ko masu alaƙa aikata laifukan yaki a kan Falasdinawa,” in ji Rana Sanaullah, mai bada shawara kan harkokin siyasa ga Firayim Ministan kasar.

Sanaullah ya kuma shaida wa manema labarai a Islamabad, babban birnin Pakistan cewa “kasar za ta yi amfani da duk wata hanya mai kyau don taimakawa Falasdinawa tare da yin Allah wadai da Isra’ila a matsayin kasar ‘yan ta’adda”.

Tare da Al Jazeera