Kasuwanci

Ƙasar Mexico ta ki amincewa ta sanyawa Rasha takunkumin tattalin arziki

Shugaban kasar Mexico

Shugaban kasar Mexico Andres Manuel Lopez Obrador ya bayyana a ranar Talata cewa, kasar Mexico ba za ta kakaba wa Rasha takunkumin karya tattalin arziki ba saboda mamaye kasar Ukraine.

Ya kuma soki abin da ya kira sanya ido kan kafafen yada labarai da gwamnatin Rasha ke daukar nauyin kamfanonin sadarwar.

Lopez Obrador ya shaidawa wani taron manema labarai cewa “Ba za mu dauki wani nau’i na ramuwar gayya ta tattalin arziki ba, domin muna son kulla kyakkyawar alaka da dukkan gwamnatocin duniya.”

Advertisement

Matsayin Lopez Obrador ya sha bamban da manyan takunkuman da kasashen duniya suka kakaba wa Rasha saboda ayyukan shugaba Vladimir Putin.

Kasar Rasha dai ta kulla alaka mai karfi da gwamnatoci daban-daban a yankin Latin Amurka, musamman ma gwamnatocin kama-karya a Cuba, da Venezuela da kuma Nicaragua, amma ana ganin alakar ta da Mexico ba ta da iyaka, saboda alaka mai karfi tsakanin Amurka da Mexico.

Advertisement